Badariyya labari ne da ya shafi soyayya, rayuwar iyali, buri, da kuma irin zaɓukan da mutum kan yi a lokacin da rayuwa ba ta ba shi isasshen lokaci ba.
Badariyya ’yar shekara 29 ce, wadda ta yi karatun jami’a inda ta samu digiri a fannin Biochemistry. Bayan kammala karatunta, ta gina kanta tare da samun nasara wajen koyar da girke-girke a kafafen sada zumunta. Yayin da yawan mabiyanta ke ƙaruwa, haka ma burinta na buɗe makarantar koyar da girke-girke ta zamani ke ƙara girma. Burinta shi ne ta gina rayuwar da ta zaɓa wa kanta, ta kuma dogara da ƙoƙarinta wajen cimma burinta.
Sai dai duk waɗannan tsare-tsare sun shiga cikin wani sabon hali bayan mahaifinta ya ba ta wa’adi: tana da kwanaki sittin kacal ta nemo mijin da za ta aura, ko kuma shi da kansa ya zaɓa mata wanda za ta aura.
Yayin da kwanakin wa’adin ke raguwa, Badariyya ta tsinci kanta a tsakiyar buri, al’ada, soyayya da kuma ’yancin yanke shawarar rayuwarta da kanta. A gefe ɗaya, tana son ta cigaba da gina rayuwar da ta yi mafarki a kanta; a ɗaya gefen kuma, tana fuskantar matsin lamba daga iyaye da al’adar da ke ganin lokaci ya yi da za ta yi aure.
Yayin da take fuskantar waɗannan manyan zaɓuka da za su iya sauya makomar rayuwarta, Badariyya dole ta gano abin da ya fi muhimmanci a gare ta, abin da take shirin ta sadaukar, da kuma irin farashin da za ta biya domin ta cimma burinta.
Ku biyo Badariyya a wannan tafiyar yayin da take neman gano wacece ita, burikanta da kuma tambayar da ke tsakiyar wannan labari: Idan makomarka ta zo da wa’adi, waye ke da ikon yanke abin da zai biyo baya?
Badariyya shiri ne da ya ta’allaƙa kan soyayya,rayuwar iyali, buri da kuma irin zaɓukan da mutum ke yi lokacin da al’ada da burikan mutum suka ci karo da juna. Labarin na biye da Badariyya yayin da take ƙoƙarin gina sana’a da makomar rayuwarta, a lokaci guda kuma tana fuskantar matsin lamba daga iyayenta da kuma wa’adin lokaci da ba ta yi tsammani ba.
Tattaunawa cikin girmamawa tsakanin ma’aurata yana taimakawa wajen gina zama na amana da fahimtar juna, hakan na taimaka musu su haɗa kai wajen magance matsalolin da suke fuskanta.
Kyakkyawar tattaunawa na ƙara inganta zamantakewa kuma ta taimaka musu wajen yanke shawarar da ta shafi iyalinsu tare.
A zaɓi lokacin da kowa yake cikin nutsuwa, a saurari juna da kyau, a guji ɗora wa juna laifi, sannan a mayar da hankali wajen neman mafita tare. Idan ana mutunta ra’ayin juna yayin tattaunawa, kowa zai samu damar faɗin abin da yake tunani, kuma hakan zai taimaka wajen hana rashin fahimta rikiɗewa zuwa rikici.
Ware lokaci na yin hira a kai a kai, ko da na ‘yan mintuna ne a kowace rana, na iya taimaka wa ma’aurata su ƙara kusanci. Tambayar juna yadda ake ciki, bayyana abubuwan da ke damun mutum cikin sakin rai, da kuma tallafa wa juna na iya ƙarawa dangantakarsu ƙarko, musamman a lokutan da ake fuskantar ƙalubale.
Yanke shawara tare na taimaka wa kowanne daga cikinsu ya ji cewar ana sauraron sa, ana mutunta sa, kuma yana da hannu a cikin abubuwan da suka shafi iyalin. Tattauna batun kuɗi, tarbiyyar yara da kuma rayuwar da zasu fuskanta a gaba na iya taimaka musu su samu mafita mai kyau kuma su ƙara ƙarfin dangantakar da ke tsakaninsu.
Ku yi ƙoƙarin zaɓar lokaci da wurin da ya dace ku yi magana cikin nutsuwa ba tare da wani abu ya ɗauke hankalinku ba. Faɗawa juna gaskiya, nutsuwa da mutunta juna na iya sauƙaƙa tattauna abubuwan da suke da wahala, ya kuma taimaka tattaunawar ta zamo mai ma’ana.
Magance rashin fahimta yana farawa ne da sauraron juna da kyau, yin tambayoyi domin a fahimci abin da ake nufi, da kuma guje wa yin zato. Mayar da hankali kan matsalar da ake son warwarewa maimakon ɗora wa juna zargi na iya taimaka wa ma’aurata su samu mafita kuma su sake fahimtar juna.
Daga cikin irin waɗannan ɗabi’u akwai mutunta juna, ɗaukar nauyi, gaskiya da riƙon amana, haɗin kai da kuma tallafa wa juna. Irin waɗannan ɗabi’u na taimaka wa wajen samar da yanayin zaman lafiya a gida da kuma ƙara danƙon dangantaka cikin iyali.
Raba nauyin ayyukan gida na iya rage wa mutum ɗaya yawan damuwar da ke kansa, tare da ƙarfafa haɗin kai a cikin gida. Idan kowa a cikin iyali na taimakon juna, hakan na iya ƙara danƙon zumunci da kuma sa rayuwar gida ta kasance cikin daidaito.
Iyali na iya ƙarfafa haɗin kai ta hanyar raba ayyukan gida, tallafa wa juna wajen cimma burin kowa, da kuma haɗa kai wajen magance matsaloli. Ƙananan abubuwan da ake yi tare za su taimaka wajen ƙara mutunta juna da ƙara danƙon zumunci.
Mutunta juna na taimaka wa kowane mutum a gidan ya ji cewar an daraja shi kuma ana sauraron sa. Idan ana mu’amala da juna cikin kyautatawa da sanin ya kamata, hakan na taimakawa wajen samar da yanayin zaman lafiya da taimakon juna a cikin gida.
Iyali za su iya taimaka wa juna ta hanyar ƙarfafa wa juna gwiwa, su tattauna yadda kowa ke son cimma burinsa, raba ayyuka da nauye-nauyen gida, da kuma samar da yanayin da kowanen su zai samu damar koyo, cigaba da kuma kokarin cimma burikansa.
Iyali na iya taimaka wa juna wajen ci gaba ta hanyar murna da nasarorin juna, ƙarfafawa juna wajen neman ilimi, ba da ƙwarin gwiwa idan an fuskanci matsala, da kuma taimaka wa juna wajen koyon sabbin abubuwa.
Tsara manufofi a bayyane kuma waɗanda zasu yiwu na ɗora mutum a hanya da kuma ba shi ƙwarin gwiwar cimma burinsa.
Rarraba manyan burirrika zuwa ƙananan matakai da za a iya cimmawa na iya taimaka wa mutum ko iyali su rika samun ci gaba a hankali.
Tsara yadda za a tafiyar da kuɗi na taimaka wa iyalai wajen kula da abubuwan da suke kashe kuɗi a kansu, a yi tanadi don abubuwan da ba a yi tsammani ba, da kuma don buƙatun gaba. Hakan na kuma taimaka musu wajen yanke shawarar yadda za su yi amfani da kuɗin a harkokin gida.Yin kyakkyawan tsare- tsare na taimakawa wajen daidaita al’amura da kawo kwanciyar hankali.
Iyali na iya inganta yanayin kashe kuɗaɗensu ta hanyar tsara kasafin kuɗi, fifita abubuwan da suka fi muhimmanci, yin tanadi a kai a kai, da kuma tattauna batutuwan kuɗi tare. Yin tanadi, sannu a hankali na iya taimakawa a samu wadatuwar kuɗi a gaba.
Tattaunawa a bayyane game da kuɗi na taimaka wa iyali su fahimci abin da kowa yake tsammani, su shirya abubuwan da za su buƙata a gaba, kuma su yanke shawara tare bisa bayanan da suka dace. Bayyana halin da ake ciki na kuɗi ga juna na kuma iya rage rashin fahimta da kuma sa kowa ya san abin da yake da haƙƙi a kai.
Rubuta da bibiyar abubuwan da ake kashe kuɗi a kai, tsara abin da ake son tarawa, fifita abubuwan buƙata a kan abubuwan sha’awa, da kuma duba kasafin kuɗi lokaci-lokaci na iya taimaka wa iyali su yi amfani da kuɗin da suke da shi yadda ya kamata, tare da shiryawa game da abubuwan da za su zo a gaba.
A halin yanzu, masu amfani da layin Airtel ne kaɗai za su iya amfani da wannan sabis. Za ku iya kiran sabis ɗin har sau 10 a kowane wata ba tare da biyan kuɗi ba. Amma daga kira na 11, za a riƙa cire kuɗin kira bisa tsarin kuɗin kiran Airtel na yau da kullum. A farkon kowane sabon wata, za a sake ba ku damar yin kira 10 kyauta. Da zarar kuka fara amfani da wannan sabis, hakan na nufin kun fahimci waɗannan sharuɗɗa kuma kun amince da su.
Ku kasance tare da Badariyya, daddaɗan, ƙayataccen shirin nan mai nishaɗantarwa. Ku more kallon shirin a duk lokacin da kuke so a tashar Arewa 24. Kuma ka da ku manta, ana kawo muku sabon shirin duk ranar Lahadi da ƙarfe 8 na dare.
Kada ku tsaya a sauraron shirin kawai, ku yi mu’amala da duniyar Badariyya. Ku shiga cikin tattaunawar tare da sauran mutane a yau.
Idan labaran da ku ka ji sun yi kama da abubuwan da kuke fuskanta a rayuwarku, kuma kuna buƙatar ƙarin bayani ko tallafi, za ku iya yin magana cikin sirri da ƙwararren mai bada shawara.
Sharuɗɗa da Ƙa’idojin Amfani da Sabis ɗin IVR
A halin yanzu, masu amfani da layin Airtel ne kaɗai za su iya amfani da wannan sabis. Za ku iya kiran sabis ɗin har sau 10 a kowane wata ba tare da biyan kuɗi ba. Amma daga kira na 11, za a riƙa cire kuɗin kira bisa tsarin kuɗin kiran Airtel na yau da kullum. A farkon kowane sabon wata, za a sake ba ku damar yin kira 10 kyauta. Da zarar kuka fara amfani da wannan sabis, hakan na nufin kun fahimci waɗannan sharuɗɗa kuma kun amince da su.